Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kwamitin da gwamna Abba Kabir Yusif ya kafa na tantance sabbin ma’aikatan da gwamnatin Ganduje ta dauka aiki ya ce ba gaskiya bane cewa basa tantance ma’aikatan da basu taba karbar albashi ba.
“A kwamitin ce mun bada sanarwar duk mutumin yake cikin mutane dubu 10 da tari takwas da gwamnatin baya take iƙirarin ta dauka aiki, mun ce ya zo mu tantance shi, Amma ba mu ce wani kar yazo gaban kwamitin mu ba saboda wani dalili”.

Da yake zantawa da Premier Radio dake kano, Mamba a kwamitin tantacewar kuma mai taimakawa gwamna Abba Kabir Yusif kan yada labarai Jamilu Abubakar Danbatta, ya ce koda mutum bai taba karbar albashi ba matukar yana da takardar daukar aiki zasu tantance shi.
Da dumi-dumi: Gwamnatin Kano ta rage kuɗin manya makarantu mallakinta
Jamilu Dambatta yace sun daga fara aikin su sun tantance wadanda akace an dauka aiki daga ma’aikatu daban-daban kuma babu wanda suka ce kar ya zo gaban kwamitin saboda wani dalili.
” Lokaci da muke aikin tantancewar mun ci karo da mutanen da aka ce ana dauke su aiki da digirin Amma albashin mai NC E ake biyansu, haka mun sami wanda aka ɗauka da NCE Amma albashin mai Digiri ake biyansa, mun ma sami wadanda wadanda an basu payslip na wata biyu amma ba’a taba basu ko sisin koba ba”. A cewar Jamilu Danbatta.
Tunda fari dai sabbin ma’aikatan ne suka zargi kwamitin da kin tantance wadanda basu taba karbar albashi ba duk kuwa da cewa sun cika ka’idojin tantancewar.