Shari’ar zaɓe: Gwamnatin Kano ta Magantu kan Cin hancin da aka yi yunkurin baiwa alƙaliya

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana damuwarta kan koken da shugabar kotun sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin jihar Kano da ta tarayya Hon. Mai shari’a Flora Ngozi Azinge ta yi, Inda ta ce wani babban Lauya ya yi yunkurin bata cin hancin kudi domin ta yi hukuncin da zai dadawa wanda yake karewa.

 

Kadaura24 ta rawaito mai Shari’ar ta bayyana haka ne a gaban kotu ya yin wani zama da tayi ranar Talata a Kano, inda alƙaliyar kotun ta koka da yadda manyan lauyoyi ke aikata rashin da’a a kotun.

Talla

Ko da yake ba ta bayyana sunan babban lauyan ba, Ms Azinge ta ce SANn din da ake magana a kai yana daga cikin masu kare wadanda ake shari’arsu a gaban kotun.

Yanzu-Yanzu: Tinubu ya raba Ma’aikatu ga Ministocinsa

Sai dai a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Baba Halilu Dantiye, ya fitar a ranar Larabar da ta gabata, ya ce gwamnati ta yi matukar damuwa akan batun, sannan akwai jita-jita mai karfi da ke cewa wasu masu karfin fada aji a cikin jam’iyyar APC, idanunsu na kan zaben Kano inda suka dukufa wajen ganin an maimaita abin da suka yi a Shari’ar zaɓen 2019.

Ya ce dukkansu a shirye suke su yi amfani da duk wata hanya da za a bi wajen yin an yi rashin adalci kamar yadda aka yi a baya.

Alƙaliyar Kotun Sauraren Kararrakin Zabe a Kano ta Koka bisa yunkurin wani Babban Lauya na bata cin-hanci

‘’ Hankalin gwamnatin jihar Kano ya karkata ne kan zargin da shugaban kotun sauraron kararrakin zabe na majalisar dokokin jihar Kano Mai shari’a Flora Ngozi Azinge, inda ta ce an yi yunkurin bata cin hancin kudi domin ta yi rashin adalci a wata shari’a dake gaban kotun da take jagoranta Inda ta ce “kudi na yawo a cikin kotun.” inji Dantiye

“Abu ne bayyane yadda wadannan mutanen da suka shahara wajen cin hanci da rashawa su aiki tukuru domin ganin a kwacewa al’ummar jihar Kano abun da suka zaba da hannayensu,” inji sanarwar.

“Duk da haka, gwamnati ta yi farin ciki da matakin da shugaban kotun Mai shari’a Flora Ngozi Azinge ta dauki na kin karɓar cin hancin, wanda hakan ke nuna cewa har yanzu akwai na gari a bangaren shari’ar Najeriya kuma akwai alkalai masu gaskiya a kasarmu.”

Gwamnatin jihar ta kuma godewa mutanen Kano da suka zabi jam’iyyar NNPP da kuri’u sama da miliyan daya a lokacin da ba ta da karfin gwamnatin tarayya, jiha, kananan hukumomi da kuma kudi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...