Daga Abdullahi Umar
Alhaji Salisu Abubakar Khiddir, Ma’ajin Babba na kasar Hausa ya yaba rawar da malaman addinin musulunci na Nigeria suka taka wajen shawo kan sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhoriyyar Nijar har suka yarda zasu zauna zama sulhu da Kungiyar ECOWAS.
” Allah ne ya kara nunawa duniya muhimmanci da darajar Malamanmu, wadanda suka warware matsalar da barazana da bakin bindiga ta kasa warwarewa, hakan ya kara nuna kimar malaman mu”.

Alhaji Salisu Abubakar Khiddir wanda wakilin ne ga Mai Martaba Sarkin Daura ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakilin Kadaura24 a kano.
Shari’ar zaɓe: Gwamnatin Kano ta Magantu kan Cin hancin da aka yi yunkurin baiwa alƙaliya
Ma’aji Babba na kasar Hausa yace wannan nasara da malaman suka Samar ba ta samu ba sai da suka hada kansu wajen ajiye banbancin akida da fahimaya, Kuma “Babu shakka da zasu cigaba da hade hankansu wallahi Babu abun da zasu sanya a gaba ba su sami nasara ba”
Juyin Mulki: ECOWAS ta Magantu kan batun Gurfanar da Bazoum a gaban kotu
” Dama mu mun dade da Sani malamai suna da kima kawai rashin hade kansu ne yake jawo matsalolin da har jahilai wadanda basu Kai ba suke fada musu maganganun da basu dace ba, amma idan suka sassauta sukar junansu za’a sami daidaito kuma jahilai su daina cin zarafinsu”. Inji Ma’aji Babba na kasar Hausa
Basaraken ya kuma bukaci yan siyasa da su daina Sanya Malamai a cikin harkokin su na siyasa, suma kuma malaman ya ce bai dace su rika amfani da wuraren karatunsu da mumbarinsu wajen shiga sha’anin Siyasa don kaucewa wulakanci.