Yaƙin da ECOWAS ke shirin yi da Nijar zai iya jefa Africa cikin mawuyacin hali – Sanata Shehu Sani

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Tsohon sanatan kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya ce babu wata doka a Africa da ta bada dama ga kungiyar raya kasashen Africa ta yamma ECOWAS tayi amfani da karfi wajen murkushe wata kasa a fadin Africa.

 

Sanata Shehu Sani ya bayyana hakan a wajen taron nuna kin jinin amfani da karfin soji wajen dawo da mulkin dimokaraddiya a jamhuriyar Niger, wanda hukumar cibiyar bada horo da bincike kan dimokaradiyya ta Mumbayya da ke kano ta shirya a jihar.

 

Ya ce idan akace za’a dau matakin yaki tsakanin ECOWAS da sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar, to gaba daya yankin Africa zai shiga wani hali na kakanakayi.

Alƙaliyar Kotun Sauraren Kararrakin Zabe a Kano ta Koka bisa yunkurin wani Babban Lauya na bata cin-hanci

“Anyi juyin mulki a kasar Burkinafaso, da kasar Gini, da Mali mai yasa ECOWAS ba suyi amfani da karfin soja wajen murkushe wadancan Sojojin ba sai a Niger, don haka bama goyon bayan matakin amfani da karfin soji akan Jamhoriyyar Nijar”. A cewa Shehu Sani

Talla

“bai kamata a ce Shugaban kasa Bola Ahmad Tunibu ya zama dan barandan America da Faransa ba, bai kamata a ace Shugaban kasa ya Tunibu ya saka yan Najeriya a cikin yakin da suke shirin farawa ba, kada kuma Bolan yayi sanadiyyar lalata doguwar alakar dake tsakanin Niger da Najeriya.” Inji shi

Wata kungiya mai zaman kanta a Arewa, ta karrama hadimin Ganduje, Aminu Dahiru Ahmad

A jawabinsa Amb. Ibrahim wayya Shugaban gamayyar kungiyoyin fararen hula na jihar Kano, ya ce wannan hali da Niger ke ciki ba karamar illa take yiwa Najeriya ba, idan akayi duba da dunbin asarar da a keyi a dukkan satin duniya.

 

“Sama da Naira Biliyan goma sha uku Yan kasuwar arewa suke asara a dukkan bako, baya ga sama da madaukan kaya (kwantaina) dubu, da suka makale a bakin bodojin Niger, dauke da kayayyaki da yanzu haka rahotanni ke cewa sun fara masu lalacewa”. Inji Ibrahim Wayya

 

Da yake nasa jawabin yayin taron masanin tattalin arzikin an Dr. Abdulsalam Kani, ya ce idan har aka sake aka fara yaƙi tsakanin kasashen Kungiyar ECOWAS da Nijar dukkanin kasashen Nigeria da Nijar zasu sami tawaya Mai yawa ta fuskar tattalin arziki.

“Dukkan wani da yake da sha’awar ya sanka hanun jari a kasashe biyun to zai fasa, saboda yakin da akeyi a tsakanin su, kuma dukkan wadanda suka sa hannun jarin ma zasu janye saboda gudun asara”. Inji Dr. Kani

 

A jawabin sa na godiya Daraktan cibiyar bada horo da bincike kan dimokaradiyya dake Mumbayya Farfesa Habu Muhammad Fagge bayan ya godewa mahalarta taron yace an shirya taron ne domin nuna kyama da kin Amincewa da kokarin da Kungiyar ECOWAS take yin amfani da karfin soji wajen warware matsalolin Kasar Nijar.

 

Taron ya sami halartar masana daga sassa daban-daban wadanda suka yi jawabai a fannonin da suka kware kan illolin da amfani da karfin soji da ECOWAS take kokarin yi akan kasar Nijar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...

Ciyaman din Wudil ya kaddamar da aikin gina magudanan ruwa a wasu garuruwa a yankin

Daga Maryam Adamu Mustapha   Shugaban karamar hukumar Wudil, Hon. Abba...