Kungiyar MACBAN ta nada Mu’azzam Pullo, Daraktan Wayar da kai, Al’adu, da Nishaɗantarwa

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Wata Kungiyar fulani mai suna Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) ta nada Ibrahim Abubakar Muazzam Pulloh a matsayin daraktan wayar da kan jama’a, al’adu da nishadantarwa sakamakon jajircewarsa na inganta zaman lafiya da kiyaye al’adun Fulani a fadin kasar nan ta hanyar wakokinsa na nishadi.

 

Shugaban kungiyar na kasa, Baba Othman Ngelzarma ne ya bayyana hakan lokaci da yake mika masa takardar shaidar kama aiki a ofishinsa da ke Abuja.

Talla

Alhaji Baba Othman ya bayyana farin cikinsa da irin rawar da shi (Abubakar Mu’azzam) yake takawa wajen samar da zaman lafiya tare da kiyaye al’adun Fulani ba kawai a Najeriya da Afirka ba har ma da duniya baki daya.

Ganduje Ya Bukaci ‘Yan Majalisun APC Na Kano Su Goyi Bayan Gwamna Abba Gida-gida

“Wannan lokaci ne da ya dace na yaba maka (Pullo) bisa rawar da kuke takawa wajen samar da zaman lafiya a tsakanin mutane daban-daban (Fulani) a fadin kasar nan da ma duniya baki daya.

“A matsayinku na matasa, muna fatan za ku ci gaba da sadaukar da kai wajen ganin al’ummarmu (Fulani), a ko’ina a duniya, don ganin sun kaurace wa duk wani abu da zai iya bata musu suna ta hanyar rungumar zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma kiyaye al’adu a duk fadin duniya.

Da dumi-dumi: Kamfanin NNPC ya Bayyana Matsayarsa Kan Batun Kara Kudin Mai Fetur a Nigeria

“An san Fulani da zaman lafiya, mutuntawa, sadaukarwa da kuma dogaro da kai ba wai a kasarmu Najeriya kadai ba, a ko’ina a duniya,” in ji shi.

Abubakar Mu’azzam Pullo daya ne daga cikin fitattun mawakan Fulfude a Kano, Gombe da sauran jihohin kasar nan da ke waka da harshensa na asali (Fulani).

Baya ga ilimin waka, Pullo ya yi aiki a kafafen yada labarai daban-daban a Kano a matsayin dan jarida, sannan ya gabatar da shirin Fulufulde a gidan Talabijin na Zamani da ke Kano, ya kuma yi aikin jarida a gidan gwamnatin jihar Kano a zamanin gwamnatin da ta gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...