Daga Halima Musa Sabaru
Kasar Kenya ta maido da wani dan karamin tallafi da ta cire domin daidaita farashin man fetur na tsawon kwanaki 30 masu zuwa a kasar.
Wannan ci gaban ya biyo bayan fushin da jama’a suka nuna kan tsadar rayuwa.
Al Jazeera ta bayar da rahoton cewa, Hukumar Kula da Makamashi da Man Fetur (EPRA), mai kula da makamashi ta Kenya, ta ce za a biya diyya ga kamfanonin sayar da man fetur daga asusun bunkasa man fetur na ƙasar.

A cewar hukumar, matsakaicin farashin litar man fetur zai ci gaba da kasancewa akan shillings 194.68 ($1.35) a wata mai zuwa, wanda zai kare masu saye daga karin shilling 7.33 ($0.05).
Ganduje Ya Bukaci ‘Yan Majalisun APC Na Kano Su Goyi Bayan Gwamna Abba Gida-gida
“Domin gudun gallazawa masu saye daga tashin farashin mai sakamakon karin kudin da aka samu, Gwamnati ta zabi daidaita farashin lita na tsawon watan Agusta zuwa Satumba 2023. Kamfanonin sayar da mai za a biya su diyya daga asusun bunkasa man fetur,” in ji sanarwar.
Bayan hawansa mulki a watan Satumba, shugaba William Ruto ya cire tallafin man fetur da na masara da magabacinsa ya yi.
Ruto ya ce ya gwammace ba da tallafin samar da mai maimakon siya.
Da dumi-dumi: Kamfanin NNPC ya Bayyana Matsayarsa Kan Batun Kara Kudin Mai Fetur a Nigeria
Jaridar Bizpoint ta rawaito Matakin a cewarsa Ruto, yana nufin rage kudaden da gwamnati ke kashewa yayin da ta ke kuma kokarin ganin ta shawo kan matsalar biyan basussukan da ya tilasta mata karyata rade-radin da ake yi a kasuwa game da cire tallafin.
Amma rage tallafin da kuma karin haraji na baya-bayan nan ya kara tsadar rayuwa tare da ba da gudummawa ga zanga-zangar adawa da gwamnati a ‘yan watannin nan.