Daga Kamal Yahaya Zakaria
Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Ganduje a ranar Litinin ya bukaci ‘yan majalisar dokokin jihar Kano su 14 na jam’iyyar da su marawa gwamnan jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf baya domin cigaban jihar.
Abba Kabir Yusuf wanda shi ne gwamnan jihar kano a jam’iyyar adawa ta NNPP , sun adawar siyasa da tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje.

Sai dai yayin da ya karbi bakuncin ‘yan majalisar a wata ziyarar taya murna da suka kai masa a gidan ‘Buhari House’ inda nan ne Sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa, Ganduje ya ce goyon bayan gwamnan jam’iyyar adawa ba zai hana su kasancewa ‘yan APC.
“Hakan ba zai hana ku ci gaba da rike matsayin ku na ‘yan majalisar jiha ba, bai hana mu hada kai don samun gwamnatin APC a jihar Kano ba. Abu mafi muhimmanci shi ne al’ummar jihar Kano su samu ribar dimokuradiyya”. Inji Ganduje
Yan sanda sun kama mutane 6 da ake zargi da yin kalaman da basu dace ba ga Sarkin Kano
“Ina so ku yi aiki da gwamnati cikin lumana a jihar Kano, ina kuma tabbatar muku da cewa za mu ba ku kwarin guiwa ta yadda za mu samu karin ‘yan majalisar dokokin jihar da ma har sai mun samu gwamnan jam’iyyarmu.
“Ina taya ku murnar lashe zaben ku da kuma yadda kuka taimaka wa shugaban kasa ya ci zabensa. Shugaban kasa ya nuna ya zuwa yanzu yana daukar jihar Kano da muhimmanci ta hanyar goyon bayan mataimakin shugaban majalisar dattawa daga Kano, ministoci biyu ya nada, sannan muka sami Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisa, uwa uba kuma ya dauko Shugaban Jam’iyya ya bamu, kun ga wannan kadai ya Isa ya nuna muku yadda Shugaban ƙasar ya bamu a Kano, domin ya san idan ya na neman kuri’a a lokacin zabe zai iya zuwa Kano,” inji shi.