Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Kamfanin kula da albarkatun man fetur na kasa NNPC ya bayyana cewa bashi da wani shiri na Kara kudin litar man fetir a Nigeria.
Idan za’a iya tunawa a makon da ya gabata wasu kafafen yada labarai a Nigeria sun rawaito cewar akwai yiwuwar za’a Kara litar man fetir daga Naira 620 zuwa Naira 720 .

Kadaura24 ta rawaito kamfanin NNPC ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a sahihin shafin sa na Twitter.
Ganduje Ya Bukaci ‘Yan Majalisun APC Na Kano Su Goyi Bayan Gwamna Abba Gida-gida
“Ya ku abokan huldar mu, mu kamfanin NNPC ba mu da wani kudiri na kara kudin man fetur a Nigeria, kamar yadda wasu suke ta yadawa jita-jita. Ku cigaba da sayan ingantaccen man da muke kawo muku cikin farashin da kuka Sani Mai sauki a duk gidajen mai dake fadin Nigeria”. Inji NNPC
Kamfanin ya bukaci al’ummar Nigeria da su yi watsi da waccen jita-jita da ake yadawa saboda ba ta da tushe ballantana makama.