Daga Hafsat Lawan Sheka
Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane shida da ake zargi da kalaman batanci ga Sarkin Kano, wanda hakan ya haifar da damuwa a wajen taron bude Asibitin Asiya Bayero dake Kano.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Hussaini Gumel ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Litinin a Kano.

Gumel ya ce wadanda ake zargin sun tayar da hankulan al’umma ne a lokacin kaddamar da asibitin yara na Hasiya Bayero da ke Kofar Kudu a karamar hukumar mulki ta jihar.
Ƴan majalisa a Ghana sun gargaɗi shugaban ƙasar kan tura sojoji Nijar
Ya ce wadanda ake zargin sun hargitsa taron ta hanyar yin wasu kalamai da basu dace ba kan mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da ya halarci bikin.
A cewarsa, wadanda ake zargin suna an kama su ne saboda yadda suke cewa “Sabon Gwamna, sabon sarki,” inda suka dage cewa Gwamna Abba Yusuf sai ya tsige Aminu Ado Bayero ya nada wani sabon Sarkin, tunda an samu sabuwar gwamnati.
Juyin Mulki: ECOWAS ta Magantu kan batun Gurfanar da Bazoum a gaban kotu
Gumel ya ce, ‘yan sanda sun yi amfani da fasaha wajen zakulo wadanda ke da hannu a lamarin, inda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike don gano wasu da ake zargi da kuma wadanda suka dauki nauyinsu.
“Ba a gayyaci wannan rukunin mutanen zuwa taron ba, kawai kutse suka yiwa taron, kuma tabbas wani ne ko wasu suka dauki nauyinsu”.
An gano mutane shida. Mun yi amfani da fasaha don gano su. Har yanzu muna nazarin faifan bidiyon, kuma muna kokarin kama duk wadanda ke da hannu a lamarin.
“Muna kuma kokarin kamo masu daukar nauyin.