Daga Auwal Alhassan Kademi
Hedikwatar tsaron Nigeria ta musanta wani rahoto mai tayar da hankali dake cewa wasu mutane sun bukaci rundunar sojojin Najeriya ta gudanar da juyin mulki a kasar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na tsaro, Brig.-Gen. Tukur Gusau, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.

Gusau ya ce rundunar sojin kasar ba ta taba samun irin wannan bukatar daga ɗai-ɗaiku ko wata kungiya ba.
“Mun yi imanin wannan magana ta fito ne daga wadanda ba sa fatan alheri ga al’ummar Nigeria.” (NAN)