Ku nemi sana’a kar ku jira aikin gwamnati – Falakin Shinkafi ya fadawa Matasa

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Amb. Dr. Yunusa Yusuf Hamzu Falakin Shinkafi ya yi kira ga matasa da su yi amfani da ilimin dasu ke da shi wajen koyan sana’o’in dogaro da kawunan su, ba su dunga zaman jiran aikin gwamnati bayan sun kammala karatu ba.

 

” Yanzu gwamnati ba ta da aikin da zata baiwa matasa don haka mafita a gare ku kawai ita ce ku rungumi sana’o’in don ku dogara da kawunanku, kuma kar kuce dole sai babbar sana’a”.

Talla

Falakin Shinkafi, ya bayyana hakan ne yayin taron da kungiyar daliban da suka gudanar da sanin makamar aiki a gidan Radio tarayya Pyramid FM Kano.

Dalilai Guda 10 da DSS ta bayar kin Amincewa da El-Rufai a matsayin Ministan Tinubu

Falakin ya ce duba irin wayan daliban da su ke gama karatu duk shekara, ba zai yiwu ba a ce duk wanda ya gama karutu ya samu aikin gwamnati ba, saboda karancin guraban aikin ga gwamnatin tarayya da ta jihohi.

” Akwai matasa da dama da suka yi arziki da kananan sana’o’i kuma yanzu sun zama abun kwatace a cikin al’umma, kuma sun sami nasara ne saboda basu raina sana’o’in da suka yi ba”. Inji Falakin Shinkafi

Ƴan majalisa a Ghana sun gargaɗi shugaban ƙasar kan tura sojoji Nijar

Shi ma da yake nasa jawabin Ibrahim Yaro Dawakin Tofa, Shugaban sashin yada labarai na gidan Radio Pyramid, ya yi jan hankali ga dalibai masu son zama yan jaridu da zage dantse wajen yin aikin mai nagarta domin shi aikin jarida aiki ne wanda yake bukatar jajircewa.

” Babu wanda yake zama wani abu a duniya ba tare da ya sadaukar da kai da jajircewa akan abun da ya sanya a gaba ba, ballantana kuma aikin jarida, don haka nake baku shawarar ku sake zage damtse wajen neman Ilimi da kuma gudanar da aikin a aikace”. Inji Ibrahim Yaro

Taron dai ya samu halartar da dama daga cikin daliban da suka gama samun haron aikin jarida a Gidan Radio na Pyramid.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...