Dalilai Guda 10 da DSS ta bayar kin Amincewa da El-Rufai a matsayin Ministan Tinubu

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Zarge-zargen cin zarafin bil-Adama, maganganun musgunawa jama’a , da kuma korafe-korafe da ake zargin jami’an tsaron farin kaya (DSS) ne suka yi kan zaben tsohon Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ne yasa majalisar dattawa taki amincewa da shi

 

Ga dalilin daki-daki kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito:

 

1- Na baya-bayan nan shi ne tsokacin da ya yi a lokacin da yake jawabi ga kungiyar malaman addinin Musulunci a Kaduna bayan jam’iyyarsa ta APC ta lashe zaben gwamna a watan Maris.

Talla

2- Cin zarafin Bil Adama, daga ciki har da shari’ar da ta shafi kisan ‘ya’ya da mabiyan shugaban ‘yan Shi’a, Ibraheem El-Zakzaky, a Zariya, Jihar Kaduna, a shekarar 2015. Shari’ar tana gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta (ICC).

3- Hukumar ta SSS ta kuma zargi Mista El-Rufai da laifin damke abokan gaba na siyasa ba bisa ka’ida ba tare da kwace kadarorin da kuma lalata dukiyoyin da ake ganin na yan adawar siyasa ne.

4- Hukumar ta DSS ta kuma zarge shi da yin amfani da karfi da kuma tursasawa wajen murkushe zanga-zangar da ta kai ga kisan gilla ga ‘yan jihar da ba su ji ba ba su gani ba.

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano ta Soke lasisin duk Makarantu Masu Zaman Kansu a jihar

5- Hukumar ta DSS ta kuma yi ikirarin cewa ana zargin sa da almubazzaranci da dukiyar al’umma, cin zarafi da amana, da yin amfani da wasu makusanta, wajen cin hanci da rashawa a lokacin da yake shugabantar Hukumar Kamfanonin sayar da kaddarorin Gwamnati (BPE), da Kuma lokacin da yayi Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), da kuma Gwamnan Jihar Kaduna.

6-Yawaitar kararraki da ake tafkawa a kan Elrufai a kotunan Najeriya da sauran kasashen duniya ciki har da ECOWAS da ICC.

7- A cewar hukumar ta DSS, hukumar ta kuma zayyana wasu korafe-korafe da aka shigar a kan Malam Nasiru El-Rufai, ciki har da wanda ta ce hukumar kare hakkin bil’adama ta Musulunci ta aika wa shugaba Tinubu.

Zikirin Shekara: Majalisar Shura ta Darikar Tijjaniyya ta bayyana matsayata kan juyin mulkin Nijar

8- Malam El-Rufai ya taba bayyana Shugaban kasa Tinubu a matsayin wanda ya fi kowa cin hanci da rashawa kuma ya sha alwashin cewa ba zai taba nada irin wannan mutumin mai gurbataccen mutunci ba.

9- Hukumar ta DSS ta kuma zargi tsohon gwamnan da yiwa tsaffin jagorancinsa na baya butulci, hukumar ta ce ya marawa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo baya, mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar (wanda aka ce shi ne ya kawo shi gwamnatin Obasanjo), da kuma tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

10- Hukumar ta kuma bayar da misali da yadda yake fito da manufofin da suke gallazawa al’umma, wadanda ake zargin sun lalata rayuwar jama’a a jihar Kaduna a matsayin shaida cewa bai cancanci rike mukamin minista ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...