Daga Hafsat Lawan Sheka
Shugaban tawagar malaman Nigeria da suka Isa kasar Nijar don samar da masalaha a rikin dake shirin faruwa tsakanin Nijar da kasashen dake karkashin kungiyar ECOWAS, Sheikh Bala Lau ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da suka tattauna da shugaban kasar ta Nijar.
Kadaura24 ta rawaito a ranar Asabar din da ta gabata ne dai malaman daga kungiyoyi da dariku daban-daban na Nigeria suka tafi zuwa kasar Nijar, domin tattauna yadda za’a sami masalaha tsakanin kungiyar ECOWAS da sabbin shugabannin mulkin soji na Nijar ba tare da anyi amfani da karfin soji ba wajen warware matsalolin.

A ganawarsa da manema labarai bayan kammala taron da sukai da shugaban kasa ta Nijar, Sheikh Bala lau yace shugaban Ƙasar Nijar ya bada damar a cigaba da tattaunawa har zuwa lokacin da za’a warware matsalolin.
Dalilai Guda 10 da DSS ta bayar kin Amincewa da El-Rufai a matsayin Ministan Tinubu
” Mun shigo mun tattauna da shi tare da jami’an gwamnatinsa kuma sun bamu hadin kai, mun yi duk abun da zamu yi don mu isar da sakon hadin kai da zaman lafiya, nasiha da masalaha, addu’a muke yi Allah ya tsare Nigeria da Nijar kamar yadda yake a tarihi”. Inji Sheikh Bala Lau
Sheikh Bala Lau yace sun ji dadin yadda Shugaban ƙasar Nijar na yanzu ya karbe su da kuma irin kalaman da yayi musu wanda hakan ya nuna ya mutunta su a matsayin su na Malamai kuma ya bude kofar da za’a sulhu.
“Dama shugaban karmu na Nijeriya shi ne ya turo mu ,Kuma idan mun koma zamu sanar da shi abubuwan da muka tattauna, kuma muna rokon da shi da shugabannin ECOWAS zasu duba don su ɗauki matakan da suka kamata, kuma abun farin ciki har wadanda ba Musulmi ba a Nigeria basa goyon bayan warware matsalar Nijar da karfin soji”.
Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano ta Soke lasisin duk Makarantu Masu Zaman Kansu a jihar
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ƙarshe watan da ya gabata sojin suka hambarar da gwamnatin Muhammad Bazoum wanda hakan ne ya jawo cece-kuce har kungiyar ECOWAS ke shirin yin amfani da karfin soji don mayar da Bazoum kan karagar mulkinsa, bayan sun bayaiwa sojojin wa’adin su saki Bazoum Kuma su mayar da shi.
Tawagar Malamai daga kowanne ɓangare ne suka je ƙasar ta Nijar Inda suka hadu da wasu daga cikin malaman Kasar ta Nijar yayin ganawa da shugaban gwamnatin Mulkin Soji ta Nijar.