Yada Manufofin gwamnatin Kano ya rataya a wuyan duk wanda Abba Kabir ya bashi Muƙami – Baba Dantiye

Date:

Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya bukaci dukkan masu rike da mukaman siyasa da su hada kai da juna domin ciyar da jihar gaba.

 

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi sabon mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin yada labarai, Hon. Akibu Shehu, wanda ya kai masa ziyara tare da gabatar da takardar nada shi ga Kwamishinan.

Talla

Dantiye wanda ya bayyana jin dadinsa da ziyarar, ya ce duk wadanda aka nada nauyi ne ya rataya a wuyansa na yada manufofin gwamnatin Abba Kabir Yusuf a jihar da kasa baki daya .

Hotunan yadda ginin babban masallacin Zazzau ya rufta ana sallah

Ya taya babban mataimaki na musamman din murna tare da sanar da shi cewa kofarsa a bude take a kowani lokaci, inda ya kara da cewa ma’aikatar yada labarai aikinta shi ne yada labarai da wayar da kan al’umma game da aiyukan gwamnati.

Iftila’i Babban Masallacin Zazzau ya rufta ana sallah

Sanarwar da daraktan wayar da akan al’umma na ma’aikatar yada labarai Adamu Abdullahi ya aikowa kadaura24, yace kwamishinan ya bayyana cewa kofarsa a bude take kuma yana maraba da duk wani yunkuri na yada kyawawan manufofi da gwamnatin Abba Kabir a jihar.

Tun da farko, Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan jihar kan Harkokin yada Labarai Hon. Akibu Shehu ya ce ya je ofishin kwamishinan ne domin ya gabatar da kansa da kuma takardar nadin nasa domin ya albarkaci kwamishinan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Bam ya fashe a Kano ya hallaka wasu ya kuma jikkata wasu

Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin...

Kotu a Kano ta sami wani Tela da laifin takurawa makwabtansa da karar keken dinki

Wata kotu a Kano ta samu wani tela da...

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...