Shugaban Ivory Coast ya ce ƙasarsa za ta tura sojoji kimanin 1,000 waɗanda za su bi sahun sauran dakarun ko-ta-kwana da za su zauna cikin shirin ko-ta-kwana don tura wa Nijar.
Alassane Ouattara na jawabi ne bayan kammala taron gaggawa na ECOWAS a Abuja, inda ƙungiyar ta ba da umarnin tanadar dakarun ko-ta-kwana don tura su Nijar a ƙoƙarin dawo da aiki da tsarin mulki.

Ya ce ƙungiyar na son a dawo da shugaban ƙasar da sojoji suka hambarar da gwamnatinsa, Mohammed Bazoum a kan mulki.
Mr Outtara, ya ce sojoji daga Najeriya da Benin da sauran ƙasashe za su haɗu da na Ivory Coast don zama cikin wannan shiri.