Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Majalisar dattawan Nigeria ta tantance Festus Keyamo bayan tsohon ministar ya nemi afuwar ‘yan majalisar.
Idan dai za a iya tunawa dai majalisar ta shiga rudani sakamakon wani kudiri na neman a dakatar da tantance Keyamo, bayan da Keyamo ya bayyana a gaban majalisar domin tantancewa.

A zaman da aka ci gaba, Keyamo ya nemi gafarar kin amsa gayyatar da wani kwamitin ya yi masa a baya, inda yace su yafe masa kuma hakan ba zata sake faruwa ba.
Ina da yaƙinin Ganduje zai kai APC ga Nasara a Nigeria – Dr. Jibril Yusuf JY
Mai tsawatarwa na majalisar, Ali Ndume, ya ce kamata ya yi shugaban majalisar ya gabatar wa sanatocin tambaya kan ko majalisar ta karɓi tuban Keyamo ko sabanin haka .
Ndume ya gabatar da kudirin cewa majalisar dattawa ta amince da uzurin, inda ya nemi Keyamo ya guji sake yin duk wani abu na raina majalisar a nan gaba.
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya yi sabbin nade-naden shugabannin ma’aikatu 15
Idan za’a iya tunawa dai a bayani dai tsohon Ministan a lokacin mulkin Muhammadu Buhari ya rika fadin kalamai marasa dadi ga yan majalisar, bayan kin amsa gayyatar da suka yi masa.