Daga Bashir Hayatu Gentile.
Engr. Abdullahi Muhammad Gwarzo, tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar ACN, an haife shi ne a ranar 23 ga Satumba, 1960, a Koyar Getso, a karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano.
Engr . Gwarzo ya fara karatun firamarensa ne a shahararriyar makarantar firamare ta kwana ta Gwarzo, inda ya kammala karatunsa na firamare kuma ya samu shaidar kammala karatunsa shekarar 1977.
Ya wuce daya daga cikin makarantun aikin ilimin kimiyya na jihar Kano da ke Dawakin-Kudu, a shekarar 1982, inda ya kammala karatunsa na sakandare .

ATM Gwarzo ya samu gurbin shiga jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, Kuma ya kammala karatun digirinsa a shekarar 1988. Ya yi bautar kasa (NYSC) a tsohuwar jihar Bendel a tsakanin 1988 zuwa 1989.
Bayan kammala shirin NYSC a 1989, Abdullahi Gwarzo, ya dawo gida, ya shiga harkokin siyasa a jamhuriya ta uku, inda ya kafa sansaninsa a jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).
Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya tsaya takarar shugabancin karamar hukumar Gwarzo kuma ya yi nasara, inda ya rike mukamin tsakanin 1991-1993.
Ya kuma taba rike mukamin shugaban karamar hukumar Gwarzo, tsakanin 1997-1998 (NCPN), 2004-2007 lokacin da ya rike mukamin Shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomin na jihar kano ALGON a Jam’iyyar ANPP, sannan yayi rike shugaban karamar hukumar na riko tsakanin 2003-2004(ANPP).
An nada shi a matsayin mai ba Gwamnan jihar Kano shawara na musamman kan ayyuka na musamman a shekarar 2007. Kamar yadda ake cewa, himma bata ga rago , a shekarar 2007, a lokacin da yake kokarin ganin ya samu tikitin tsayawa takarar dan majalisar tarayya a yankin Kabo da Gwarzo a jam’iyyarsa, gwamnan Kano na wancan lokacin Malam Ibrahim Shekarau ya dauko shi a matsayin wanda zai yi masa mataimakin gwamna a jam’iyyar ANPP a zaben 2007 wanda kuma suka yi nasara Inda ya rike mukamin tsahon shekaru 4.
A dai wannan Shekarar Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya zama Shugaban tawagar alhazan jihar Kano wato Amiruj Hajj 2007, ya jagoranci jihar kano a gasar cin kofin duniya, Afirka ta Kudu, 2010, ya kuma zama jagoran tawagar jihar kano a taron tsaftar ruwan sha ta duniya, a Cordoba, Spain, 2009, sanann ya sake jagoranta jihar kano a taron noma na zamani na duniya wanda akai a Hague dake kasar Holland.
A lokacin da yake mataimakin gwamnan jihar Kano, shi ya rike ma’aikatar albarkatun ruwa ta jiha a matsayin kwamishina, inda ya kula da aikin gina matatar ruwa ta kano, mai samar da lita miliyan 75,000,000 a kowace rana, da aikin ruwa na Watari, da sake farfado da babban aikin samar da ruwan Kano, Kuma nasarar da ya samu a bangaren wadata kano da ruwan sha tasa kanawa suka rika yi masa lakabi da ‘RUWA BABA’.
Daga baya ya sauya sheka daga jam’iyyar ANPP zuwa jam’iyyar ACN, inda ya tsaya takara a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben gwamna na 2011, wanda bai yi nasara ba.
Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo shi ne kuma Shugaban Jam’iyyar APC na jihar kano na farko bayan sanar da ita a Shekara ta 2013.
Wannan gogewa da kasancewa cikin al’ummar sa a kowanne lokaci, tasa aka dade ana damawa da ATM Gwarzo a matsayin Uba Kuma jigo na jam’iyyar APC a jihar kano da kasa baki daya.
A yanzu haka dai yana daga cikin mutanen da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya dauka daga jihar kano domin nada shi a matsayin minista, Inda har Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya bayyana sunansa a matsayin guda cikin wadanda majalisar zata tantance domin nada shi a matsayin minista kuma dan majalisar zartarwar Shugaban kasa.
Yanzu haka dai al’ummar jihar kano na ta murna da Sam barka da wannan mukami da za’a nada T Gwarzon, kasancewar an hakikance cewa dan Siyasa ne da zai amfanar da al’umma ta fannoni daban-daban, sannan kuma ana da yaƙinin ba zai baiwa Shugaban kasa Bola Tinubu kunya ba, sakamakon jajircewar da yake da ita a duk abun da ya sanya a gaba.