Juyin Mulki: Najeriya ta Yankewa Kasar Nijar Wutar Lantarki

Date:

Daga Abdulrashid B Imam.

 

Najeriya ta dauki matakin katse layin wutar lantarkin da yake kaiwa kasar Nijar wuta, biyo bayan takunkumin da aka kakaba wa gwamnatin mulkin sojan kasar da ta hambarar da zababben shugaban kasar , kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya rawaito.

 

Wata majiya daga kamfanin samar da wutar lantarki na Niger Nigelec ta bayyana cewa, “Tun a jiya, Najeriya ta katse layin wutar lantarki da ke jigilar wutar lantarki zuwa Nijar.”

Talla

Nijar dai ta dogara ne da Najeriya wajen samun wutar lantarki da akalla kashi 70 cikin 100, inda ta siya daga kamfanin Mainstream na Najeriya, a cewar Nigelec, wanda shi ne ke samar da wutar lantarki a kasar.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Sabon Ministan da Tinubu zai nada daga Kano Engr. Abdullahi T Gwarzo

Dam din Kainji da ke yammacin Najeriya ne ke samar da wutar lantarkin .

Duk da cewa suna da kananan hanyoyin samun wutar a cikin babban birnin kasar Yamai, amma tuni wasu garuruwa suka fara fuskancir rashin wutar lantarkin tun ma kafin juyin mulkin.

Yanzu-Yanzu: Akpabio ya bayyana sunayen T Gwarzo, Matawalle Lalong da wasu 16 a matsayin ministocin Tinubu

Domin samun wutar lantarkinta kasar Nijar na kokarin gina madatsar ruwa ta Kandadji a kogin Neja, mai tazarar kilomita 180 (mil 110) daga Yamai.

Ana sa ran kammala aikin dam din a shekarar 2025 kuma ana sa ran samun wutar lantarki mai karfin migawatt 629 a shekara (GWh).

Firayim Minista Ouhoumoudou Mahamadou ya bayyana damuwarsa game da tasirin takunkumin, yana mai cewa, “Takunkumin zai yi wa kasarmu illa sosai,” a wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta Faransa ta France24.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...