Daga Adamu I Adamu
Sabbin shugabannin mulkin soja a kasar Nijar da suka karbi mulkin kasar a cikin ‘yan kwanaki da suka gabata sun tsare akalla jami’an gwamnatin da aka hambare ta dimokuradiyya dari da tamanin (180), kamar yadda jam’iyyarsu Bazoum ta bayyana a ranar Litinin.
Shugaban jam’iyyar dimokradiyya da gurguzu ta Nijar, Foumakoye Gado, ministan ma’adinai, Ousseini Hadizatou da ministan makamashi, Mahamane Sani Mahamadou na daga cikin wadanda aka tsare, in ji kakakin jam’iyyar Hamid N’Gadé.

N’Gadé ya kara da cewa, Ministan Sufuri, Oumarou Malam Alma da mataimakinsa, Kalla Moutari, ciki har da ministan harkokin cikin gida, Hama Adamou Souley, suma masu yunkurin juyin mulkin na tsare da su, kamar yadda NAN ta ruwaito.
“Kame da ake yi” shaida ne na “halayen danniya, kama-karya da kuma gwamnatin haramci da sojojin Nijar suke yi”, in ji N’Gadé.
Da dumi-dumi: Muhimman gabobi 5 na Jawabin Shugaban Tinubu
A ranar Larabar da ta gabata ne jami’an rundunar Janar Omar Tchiani suka ayyana hambarar da zababben shugaban kasar PNDS Mohamed Bazoum na jam’iyyar PNDS . Daga baya Tchiani ya nada kansa a matsayin sabon mai mulki a ranar Juma’a.
Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin tantace ma’aikatan REMASAB
Jim kadan bayan haka, masu yunkurin juyin mulkin sun dakatar da kundin tsarin mulkin kasar tare da rusa dukkan hukumomin tsarin mulkin kasar. Kasashen duniya dai sun yi Allah wadai da juyin mulkin.
Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta fitar da wa’adi ga shugabannin da suka yi juyin mulki a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta ce idan ba a sako Bazoum ba, aka maido da shi kan mukaminsa cikin mako guda, ECOWAS za ta dauki matakan da za su hada da amfani da karfi akan sojojin na kasar Nijar.