Shugaban Nigeria Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga al’ummar kasar, musamman matasan da su ƙara haƙuri kan halin matsin rayuwa da suke fuskanta a yanzu.
Tinubu ya bayar da tabbacin cewa wahalhalun da ƴan Najeriya ke fuskanta a yanzu za su zamo daɗi a nan gaba.

“Gwamnatinna za ta yi aiki tare da matasa a dukkan matakan da za ta riƙa ɗauka, ba kuma zan yi shakkun ɗaukar kowane mataki da zai kawo ci gaba da haɗin kan Nigeria ba.” A cewar Tinubu
Yanzu-Yanzu: Sojojin Nijar sun Bayyana Sabon Shugaban Kasar
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a fadar gwamnatin ƙasar yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin matasa na jam’iyar APC daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Shugaba Tinubu ya ce ya fahimci irin raɗaɗin da ƴan ƙasar ke ciki “Na yi rantsuwa ga ƙasata cewa ba zan yi shakkar ɗaukar kowane irin matakin da zai samar da ci gaba da tabbatar da haɗin kan ƙasar nan ba.
“Matakan farfaɗo da tattalin arziki kan ɗauki lokaci kafin a fara ganin alfanunsu. Ku ƙara haƙuri kaɗan.”