Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
Wasu daga cikin jarumai a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood sun fara hasashen harkar fim zata kara inganta, sakamakon yadda Gwamnan Kano ya nada kwararren jarumi a matsayin Shugaban hukumar tace fina-fine ta jihar kano.
” Abba El-Mustapha ya jima a wannan Masana’antar kuma yasan duk matsalolin mu don haka muna da tabbacin zai yi amfani da gogewa da kwarewarsa wajen inganta harkokin fina-finan Kannywood a Kano”.

Rabi’u Sani wanda ake yiwa lakabi da babban Nura shi ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayin da jaridar kadaura24 a Kano.
Ministoci: Dalilin da yasa Tinubu bai tura sunan kowa daga Kano ba
Baban Nura yace gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya yi hangen nesa wajen zabo Abba El-Mustapha a matsayin wanda zai jagoranci hukumar tace fina-fine ta jiha, Saboda yadda yasan makamar aiki ga shi kuma da jajircewa wajen tsayawa gaskiya.
” Ina amfani da wannan dama wajen ta ya Abba El-Mustapha Murnar samun wannan mukamin, sannan Ina kira a gare shi da tsaya yayi aikinsa tsakani da Allah ya kuma yiwa kowa adalci wanda idan yayi haka babu Shakka ba zamu tabawa mantawa da shi ma ko bayan ya bar mukamin”. Inji Baban Nura
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a makon da ya gabata ne gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya nada Abba El-Mustapha a matsayin Sakataren zartarwa na hukumar tace Fina-finai da dab’i ta jihar kano.