Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya sha alwashin hada karfi da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin dakile mummunar dabi’ar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.
Mai Martaba Sarkin ya bayyana hakan yayin taron wayar da kan matasa wanda kungiyar INITIATIVE FOR COMMUNITY ACTION AGAINST DRUG ABUSE ( ICAADA ) wadda ke yaki da dabi’ar shaye-shaye ta dauki nauyin taron a jami’ar Yusuf Maitama sule dake kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya ja hankali jami’an tsaro dasu kara lura da yadda matasa suke safara da shan kayan maye wadanda suke sadiyyar lalacewar rayuwar su da kuma kawo cikas ga cigaban su da jihar kano baki daya.
Shuwagabannin APC Na Arewa Maso Yamma Sun Amince Da Ganduje A Matsayin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa
Ya yi kira ga dukkanin shugabannin al’umma da su kansu al’ummar da su maida hankali wajen ganin an cigaba da wayar da kan al’ummar musamman matasa illolin shan miyagun kwayoyi.
Sojoji sun bayyana dalilan da suka sa suka yi juyin mulki a Nijar
Shi ma anasa bangaran Ahmad Abubakar yakasai yaja hankalin dalibai da su guji yin abota da abokanai masu tu’ammali da muggan kwayoyi, sannan su rika jan hankali abokansu da suke yi don su gujewa dabi’ar saboda yadda take lalata rayuwar matasa .