Sojoji sun bayyana dalilan da suka sa suka yi juyin mulki a Nijar

Date:

Sojoji sun sanar da karɓe iko a Nijar a hukumance.

Wasu sojoji ƙalilan ne suka fito gidan talabijin na ƙasar suka tabbatar da juyin mulkin da suka yi.

Kakakin sojojin ƙasar Manjo Ahmadou Abdrahamane ne ya sanar da juyin mulkin.

Sun sanar da rushe kundin tsarin mulkin ƙasar, sannan kuma sun kulle duka iyakokin ƙasar baki ɗaya.

Talla

Babu dai labarin halin da Mohamed Bazoum ke ciki ya zuwa yanzu.

Amma sojojin sun bayar da sanarwar sun tuɓe shi daga muƙaminsa.

Shuwagabannin APC Na Arewa Maso Yamma Sun Amince Da Ganduje A Matsayin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa

BBC Hausa sun rawaito sojojin sun ce sun yi juyin mulkin ne saboda halin da Nijar ke ciki na taɓarɓarewar tsaro da tattalin arziƙi.

Sun kuma sanar da dokar hana fita daga ƙarfe 10 dare zuwa 6 na safe.

Da dumi-dumi: Jami’an tsaro sun tsare shugaban Niger

Shugaban ƙasar Benin Patrice Talon wanda ke jagorantar tawagar ECOWAS na cikin ƙasar, sai dai sun gaza cimma wata yarjejeniya da masu gadin shugaban ƙasar da suka amshe mulkin.

Tun a safiyar jiya Laraba ne aka bayar da rahotannin tsare Shugaba Bazoum a gidan gwamnati, abin da ya janyo zanga-zanga daga magoya bayan Bazoum.

Sojoji sun yi harbe-harben jan kunne domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya nuna rashin goyon bayan wannan ƙasarsa kan juyin mulkin.

Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ya yi magana da Shugaba Bazoum kuma ya tabbatar masa da cewa yana da goyon bayan Majalisar.

Wannan ne juyin mulki na huɗu da aka yi a Nijar tun bayan samun ‘yancin kai da ta yi daga Faransa a 1960, kuma an ta yin yunkurin junyin mulki da yawa a ƙasar da ba su yi nasara ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...