Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres “ya yi kakkausar suka ga sauyin gwamnati da aka samu a Nijar ba bisa ka’ida ba,” in ji kakakinsa a ranar Laraba.

Mista Guterres ya ce ya damu matuka da tsare Shugaba Mohamed Bazoum kuma ya damu da lafiyarsa, in ji kakakinsa Stephane Dujarric a cikin wata sanarwa.
Da dumi-dumi: Muhammad Bozoum ya Magantu Bayan yi Masa Juyin Mulki
BBC Hausa ta rawaito hakan na zuwa ne bayan da sojojin Nijar din suka sanar da juyin mulki a gidan talabijin na kasar, inda suka ce sun jingine aiki da kundin tsarin mulkin kasar, tare da dakatar da dukkan hukumomi da kuma rufe iyakokin ƙasar.
Mista Dujarric ya ƙara da cewa “Sakatare-Janar ɗin ya yi kira da a gaggauta kawo karshen duk wasu ayyukan da ke kawo cikas ga tsarin dimokuradiyya a Nijar.”