Shugaban ƙasar Nijar, Mohamed Bazoum, wanda aka hambarar da gwamnatinsa a wani juyin mulkin da sojoji suka yi, ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa za a kare nasarorin da kasar ta samu.

Wasu gungun jami’an soji ne suka sanar da juyin mulkin a gidan talabijin na kasar a ranar Laraba da yamma tare da dakatar da dukkan hukumomin gwamnati.
Shuwagabannin APC Na Arewa Maso Yamma Sun Amince Da Ganduje A Matsayin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa
Ministan harkokin waje Hassoumi Massoudou ya yi kira ga al’ummar kasar da su yi adawa da kwace ikon da sojoji suka yi.
An dai yi Allah-wadai da juyin mulkin a wajen kasar amma abin da ba a bayyana ba shi ne yadda lamarin zai kasance a Nijar.