Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya shawarci gwamnati data amincewa hukumar kare haddura ta kasa (Road Safety) ta gudanar da aikinta ako wannen titi ba tare da takura musu ba.
Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana cewa sahhalewa hukumar ta gudanar da aikinta a kowanne titi zai karawa hukumar karfi wajen bincikar takardun motoci masu inganci da masa inganci.

Sarkin ya bayyana haka ne ayayin da yake karbar ayarin shugabanin gudanarwar hukumar kare haddura ta kasa reshen jihar kano karkashin jagorancin sabon kwamandan hukumar Alhaji Ibrahim Abdullahi Sallau a fadarsa.
Shuwagabannin APC Na Arewa Maso Yamma Sun Amince Da Ganduje A Matsayin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa
Mai martaba sarkin kano ya kara da cewa yana kira da direbobi da sauran masu ababan hawa su baiwa hukumar kare haddura cikakken hadinkai da goyon baya don samun nasarar da hukumar.
Shi ma anasa jawabin sabon kwamandan hukumar Alhaji Ibrahim Abdullahi sallau yace ya kaiwa Sarkin ziyarar ne domin gaisuwar bangirma da gabatar da kansa a matsayin sabon kwamandan hukumar FRSC.
A wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24, yace a wani cigaban kuma Mai Martaba Sarkin ya karbi bakoncin shugabanin gudanarwar Bankin musulinci na Jaiz Bank karkashin jagorancin shugaban gudanarwar bankin Alhaji Muhammad Mustapha Bintube a fadarsa.