Shuwagabannin APC Na Arewa Maso Yamma Sun Amince Da Ganduje A Matsayin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Kungiyar shugabannin jam’iyyar APC reshen arewa maso yamma ta amince da tsohon gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

 

Hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Abdullahi Abbas, shugaban APC na Kano; Hon. Isa Sadiq Acid, shugaban jam’iyyar APC a jihar Sokoto; Air Cdre. EK Jekada, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kaduna, Hon. Abubakar Muhammad Kana, shugaban jam’iyyar APC a jihar Kebbi; Hon. Tukur Umar Danfulani, shugaban jam’iyyar APC a jihar Zamfara; da Hon. Aminu Sani Gumel, shugaban jam’iyyar APC na jihar Jigawa.

Talla

Shugabannin sun ce sun dauki matakin ne saboda Dr Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya yi wa’adi biyu a matsayin gwamnan jihar Kano, ya bayar da gudunmawa sosai ga jam’iyyar musamman a zaben 2023.

 

Sun jaddada cewa, a lokacin yakin neman zaben shugaban kasa na 2023, Dr Ganduje ya zagaya kusan dukkan jihohin tarayyar kasar nan, inda aka samu fitowar shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Najeriya.

Da dumi-dumi: Jami’an tsaro sun tsare shugaban Niger

A wata sanarwa da Aminu Dahiru Ahmad
mai hoton tsohon gwamnan Ganduje ya bayyana cewa suma tsofaffin gwamnonin jam’iyyar APC sun fara zuwa domin nuna goyon bayan su ga tsohon gwamnan na kano a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa.

Wata kungiyar mai zaman kanta ta AHIP, ta fara shirin inganta ilimin ‘ya’ya mata a Kano

Yace wadanda suka ziyarci Gandujen sun haɗar da Tsohon gwamnan Kaduna Nasiru Ahmad El-Rufai, da tsohon gwamnan Niger Abubakar Sani Bello, tsohon gwamnan Zamfara Bello Muhammad Matawalle da dai sauransu.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a farkon makon nan ana ta rade-radin Shugaban kasa Bola Tinubu ya cire sunan Ganduje daga cikin wadanda za’a baiwa mukamin Minista domin bashi rikon mukamin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa , bayan da tsohon shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu yayi Murabus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...