Daga Rahama Umar Kwaru
Kwamishinan ilimi na jihar Kano Alh. Umar Haruna Doguwa ya umurci daraktocin ma’aikatar da hukumomin dake karkashin ta da su rungumi fasahar zamani, domin tabbatar da ingantaccen tsarin tafiyar da harkokin ilimi a jihar.
Ya ce dole ne masu kula da sha’anin ilimi su rungumi fasahar zamani don tafiyar da ma’aikatar dai-dai da zamani.

Alh.Umar Doguwa ya yi wannan kiran ne a lokacin bude taron bita da jami’ar Skyline, wata jami’a mai zaman kanta da ke Kano ta shirya wa shugabannin ma’aikatar.
Yadda Kansiloli suka dakatar da shugaban karamar hukuma a Kano
“Muna cikin zamani na fasahar sadarwa kuma ba za mu yarda a bar mu a baya ba. Abubuwa sun canza sosai kuma an sami sauyi a al’amura da dama don haka dole mu karɓi canjin don gudun kar a bar mu a baya, ”in ji shi.
Majalisar dokokin Kano ta kaddamar da kwamitoci 38
Kwamishinan ya jaddada cewa dole ne ma’aikatan gudanarwa na ma’aikatar sa su rungumi kyakkyawan tunani da kuma fasahar zamani don inganta harkokin Ilimi da aiyuka a ma’aikatar.
Ya bayyana jin dadinsa bisa yadda Jami’ar Skyline ta shirya horon kyauta ga ma’aikatan ma’aikatar ilimi a matsayin wani bangare na gudunmawar ta kan al’amuran da suka shafi al’ummar da aka samar da jamai’ar a cikinsu, tare da yin fatan jami’ar zata cigaba da gudanar da aiyukan da zasu kara darajar jihar kano.
A sanarwar da daraktan wayar da akan al’umma na ma’aikatar ilimi Ameen K Yassar ya aikowa kadaura24, yace Kwamishinan ya yi fatan mahalarta taron zasu yi amfani da horon da suka samu wajen inganta aikin su da cigaban jihar kano baki daya. wanda ya kunshi fasahar zamani da horar da jagoranci zai yi amfani ga mahalarta taron kai tsaye da ma jihar baki daya.
Shugaban jami’ar Skyline ta Kano Farfesa Ajith Kumar Vadakki Veetil ya shawarci mahalarta taron da su canza tunaninsu ta hanyar karbar ilimin fasahar zamani, inda ya nuna cewa a matsayinsu na manyan ma’aikata a fannin ilimi, dole ne su kasance masu gogayya abun da ta duniya da fasahar sadarwa ke tafiya da su.