Da dumi-dumi: Kungiyar ƙwadago a Nigeria za ta fara yajin aiki a fadin kasar nan mako mai zuwa

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki bakwai na janye duk wasu tsare-tsaren da suka jefa talakawa cikin mawuyacin hali, ciki har da karin farashin man fetur da aka yi a baya-bayan nan, ko kuma ta fuskanci yajin aikin gama gari daga ranar 2 ga watan Agusta.

Talla

Kungiyar kwadago ta NLC ta umurci dukkanin rassanta dake jihohi da su gaggauta fara haɗa kan ma’aikata da sauran ’yan Najeriya da suka hada da kungiyoyin farar hula don gudanar da yajin aikin da za a dade an yi tare da zanga-zanga idan gwamnati ta gaza biyan bukatunta.

Kansilolin 11 daga karamar hukuma daya sun fice daga jam’iyyar APC a Kano

An tattaro cewa wannan na daya daga cikin shawarwarin da aka cimma a taron kwamitin koli na NLC, wanda aka gudanar a ranar Talata, 25 ga watan Yuli a gidan ma’aikata na Abuja.

Idan dai za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta sanar da karin kudin farashin man fetur daga 540 kowacce lita zuwa Naira 617 kowacce lita, wanda hakan yasa al’ummar ƙasar suke ta kokawa wasu kuma suka ajiye ababen hawansu saboda tsadar man fetur din.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta sami wani Tela da laifin takurawa magwabtansa da karar keken dinki

Wata kotu a Kano ta samu wani tela da...

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...

Ciyaman din Wudil ya kaddamar da aikin gina magudanan ruwa a wasu garuruwa a yankin

Daga Maryam Adamu Mustapha   Shugaban karamar hukumar Wudil, Hon. Abba...