Daga Halima Musa Sabaru
Jami’an tsaron fadar shugaban kasar na tsare da Mohamed Bazoum, shugaban kasar Nijar, bayan da ya sojojin Kasar suka bukaci ya sauka kamar yadda wata majiya kusa da Bazoum ta ruwaito a ranar Laraba.
Wasu daga cikin masu gadin da suka fusata sun rufe hanyar shiga gidan shugaban da ofisoshinsu, kuma bayan da tattaunawar ta kaure “sun ki sakin shugaban,” majiyar ta kara da cewa: “Sojoji sun ba su wa’adi .”

A wani sako da aka fitar a shafin Twitter, wanda ake yiwa lakabi da X, ofishin shugaban kasar ya ce “bangaren dakarun tsaron fadar shugaban kasa sun yi fushi, don haka sun shirya daukar mataki akan duk wasu son kai tarnaki kasar .”
Yadda Kansiloli suka dakatar da shugaban karamar hukuma a Kano
Sojoji da jami’an tsaron kasa a shirye suke su kai farmaki kan ‘yan ta’addar PG da ke da hannu a cikin wannan hali da ƙasar take ciki ,” inji fadar shugaban kasar.
“Shugaban da danginsa suna cikin koshin lafiya,” in ji shi.
An zabi Bazoum ta hanyar dimokiradiyya a shekarar 2021, inda ya karbi ragamar shugabancin kasar da take cikin kasashe mafi talauci a Afirka .