Yadda Kansiloli suka dakatar da shugaban karamar hukuma a Kano

Date:

Daga Abdulrashid B Imam

 

An dakatar da shugaban karamar hukumar Nassarawa, a jihar Kano Hon. Auwalu Lawan Shu’aibu daga aiki har zuwa wani lokaci.

 

Majiyar Kadaura24 ta Solacebase ta ruwaito cewa dakatar da Auwal Shu’aibu, wanda aka fi sani da Aranponsu na kunshe ne a cikin wata takarda da ta fita mai dauke da sa hannun kansiloli takwas cikin 11 na majalisar.

 

Kansilolin sun umarci shugaban da aka dakatar da ya mika ragamar shugabancin ga mataimakinsa, Hon. Muazu Abubakar Adamu kafin a kammala bincike.

Talla

A cikin wasikar dakatarwar da aka baiwa ‘yan jaridu a ranar Talata, an zargi shugaban majalisar da aka dakatar da almubazzaranci da kudade, rashin zuwa aiki, son zuciya, rashin da’a da kuma karya dokokin majalisar da dai sauransu.

 

Kansilolin sun kuma zargi Aranponsu da mika ragamar karɓar kudaden harajin na karamar hukumar ga abokinsa na kud da kud da kuma gaza aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma, ayyukan jin kai a kafatanin unguwanni dake yankin karamar hukumar.

Da dumi-dumi: Jami’an tsaron Najeriya sun ba hammata iska kan Emefiele

Kazalika, ‘yan majalisar sun zargi shugaban da karkatar da wasu kudade da aka amince da su don siyan motocin karamar hukumar da kuma yin katsalandan a cikin harkokin majalisar, wanda hakan ya haifar da rudani, hargitsi da zagon kasa.

” Gazawar ka wajen kiyaye dokoki da ka’idojin da aka tsara da kuma ka’idojin kudi da na kula da karba da fitar da kudaden majalisar karamar hukumar ta Nasarawa”. A cewar wasikar

Majalisar dokokin Kano ta kaddamar da kwamitoci 38

Da aka tuntubi shugaban karamar hukumar Hon Auwalu Lawan Shu’aibu ya shaida wa majiyar kadaura24 cewa, kansilolin ba su da hurumin tsige shi ko kuma dakatar da shi saboda tsarin mulki ba majalisar jiha kadai ya baiwa damar yin hakan kadai ba su ba.

Aranponsu wanda ya musanta zargin ya ce masu zarginsa na da wata manufa ta da ta shafi Siyasa.

“Me yasa sai yanzu suka fito a da wadannan zarge-zargen, bayan kusan shekaru biyu da rabi ba su yi ba, idan ba siyasa ba aka Saka ba,” in ji shugaban.

Shugaban ya ce ba a kai masa takardar dakatarwar ba, amma ya ga wasikar a shafukan sada zumunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...