Majalisar dokokin Kano ta kaddamar da kwamitoci 38

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

A ranar Talata ne shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Ismail Falgore, ya kaddamar da kwamitoci 38 domin gudanar da ayyukan sanya idanu ga aiyukan ɓangaren zartarwa a jihar.

 

Majalissar ta 10 ta kasance tana aiki da kwamitocin wucin gadi tun bayan kaddamar da ta a ranar 13 ga watan Yuni.

Talla

Da yake jawabi a wajen kaddamar da taron, Falgore ya ce kwamitocin za su sanya ido kan ayyukan gwamnati a matsayin cikamakon aiyukan majalisar.

 

Falgore ya ce kwamitin da ke kula da asusun gwamnati zai kasance karkashin Alhaji Tukur Fagge; Ayyuka da Gidaje, Muhammad Aliyu; Aminu Ungogo, Kudi; Ahmed Ibrahim; Noma.Sauran sun hada da, Haruna Tahir, Albarkatun Ruwa; Alhassan Ishak, Lafiya; Suleiman Ishak, Ilimi; Shuaibu Rabiu, yada labarai da Ibrahim Muhammad, Karkara; da sauransu.

Wani lauya a Kano ya nemi yan sanda su baiwa A.A Rufa’i kariya, tare da bincikar masu tunzura shi

Kakakin majalisar ya shawarci shugabannin kwamitocin da Maida hankali wajen sauke nauyin da aka dora musu.

A Wani labarin kuma majalisar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta kafa kwalejin ilimi a karamar hukumar Karaye.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na jama’a da Ahmed Ibrahim (NNPP- Karaye) ya gabatar.

Da yake gabatar da kudirin, Ibrahim ya ce kwalejin, idan aka kafa ta za ta bunkasa harkar ilimi ga al’ummar yankin da jihar da ma kasa baki daya.

Dan majalisar ya kuma bayyana cewa hakan zai kara habaka tattalin arzikin yankin tare da samar da ayyukan yi ga matasan yankin.

A tasa gudunmawar mataimakin kakakin majalisar, Alhaji Muhammad Butu-Butu, (NNPP- Rimingado/Tofa) ya ce kwalejin idan aka kafa ta za ta magance matsalar karancin malamai a yankin.

Ya kuma ce makarantar za ta samar da ayyukan yi ga al’ummar Kiru da Bebeji da Karaye da Rimingado da kuma Tofa.

Bayan zaman da ‘yan majalisar suka yi, majalisar ta amince da kudurin, kuma ta bukaci gwamnatin jihar da ta kafa kwalejin ilimi a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...