Har yanzu babu wani mutum da ya kamu da cutar Anthrax a Najeriya – NCDC

Date:

 

Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya NCDC ta ce har yanzu cutar Anthrax – da wasu dabbobin ƙasar suka kamu da ita, ba ta yaɗu zuwa ga bil-adama ba.

 

Gwamnatin Nigeria ƙarƙashin ma’aikatar lafiyar ƙasar na ƙarfafa gangamin wayar da kai kan alamomin cutar da yadda za a kauce wa ɗaukar ta, musamman a masarautar Suleja da ke jihar Naija.

Talla

gidan Talbijin na ƙasar NTA ya ambato shugaban hukumar, Dakta Nasir Ahmed na cewa hukumar na ci gaba da lura tare da sanya idanu, musamman a garin Suleja inda cutar ta fara ɓulla a ƙasar.

Mun Gano Kabilanci da Rashin Kuɗi ne yasa Fina-finan Kannywood Basa Karade Nigeria – Ado Gidan Dabino

Sarkin Suleja Muhammadu Auwal Ibrahim ya yi kira da hakiman masarautar da su kai rahoton rashin lafiyar dabbobi a yankunansu, tare da kauce wa cin naman da likitocin dabbobi ba su tantace lafiyarsa ba.

 

Tuni dai gwamnatin ƙasar ta bayyana sayen alluran riga-kafin cutar domin yi wa dabbobi a garin Suleja, inda cutar ta fara ɓulla.

Majiyar Kadaura24 ta BBC Hausa ta rawaito, Dabbobi na gida da na daji na kamuwa da cutar ne idan suka shaƙe ta daga ƙasa wadda ke ƙunshe da ƙwayoyin cutar ko kuma suka ci ciyawa ko shan ruwan da ke ɗauke da ita.

Dabbobin da suka fi kamuwa da cutar sun haɗa da shanu da tumaki da awaki da kuma barewa.

Haka kuma likitoci sun ce mutane na kamuwa da cutar a lokacin da suka yi cuɗanya da dabbobin da ke ɗauke da cutar ko kuma suka taɓa wani abu da ya fito daga jikin dabbobin.

A baya-bayan nan dai hukumomin Najeriya sun bayyana ɓuallar cutar a jihar ta Naija, lamarin da ya sa hukumomin lafiyar ƙasar yin gargaɗi game da cin naman dabbobin da ba su da lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...