Bidiyon Dala: Femi Falana Zai Tsayawa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano a Shari’ar su da Ganduje

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Hukumar Karɓar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano, ta ce fitaccen lauyan nan dan rajin kare hakkin bil’adama, Femi Falana (SAN), shi ta dauka domin taimakawa hukumar a karar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya shigar, na dakatar da binciken da hukumar ke yi kan bidiyon dala .

 

Lauyan hukumar Usman Fari ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a bayan da kotu ta dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Yuli.

Talla

Dage shari’ar ya biyo bayan kalaman lauyan Ganduje, Basil Hemba, Inda ya shaida wa kotun cewa mai karar na bukatar karin lokaci domin amsa karar da hukumar ta shigar.

Shari’ar zaɓen gwamnan Kano: Rashin bayyanar Shaidu Abba Gida-gida a Kotu yasa hana shi fara kariya

“A ranar 25 ga watan Yuli, babban lauyan nan, Femi Falana (SAN) zai jagoranci lauyoyin hukumar su shida. Hukumar ta sa shi ya jagorance mu a kan lamarin kuma a shirye muke mu ci gaba da shari’ar,” Fari ya ce yayin da yake zantawa da manema labarai.

Daily trust ta rawaito cewa da safiyar Juma’a ne aka bukaci babban lauyan ya isa Kano domin ya jagoranci tawagar amma ya samu matsala da Jirgin da zai kai shi kanon.

Idan za a iya tunawa, tsohon gwamnan ya shigar da karar ne don neman kotu ta hana hukumar hana cin hanci da rashawa ta jihar kano daga kamawa ko bincikar sa , akan batun zargin wani bidiyo da aka ga tsohon Gwamnan yana sanya dalilin a aljihunsa, wanda ake zargi cin hanci ne da wasu yan kwangila suka bashi.

A bisa wannan bukatar ce, kotun da mai shari’a A.M. Liman yake jagorantar a ranar 7 ga watan Yuli, ya amince da rokon Ganduje na ya hana hukumar yaƙi da cin hancin da rashawa ta kano, da wasu mutane bakwai gayyata ko kuma musgunawa tsohon gwamnan kan zargin cin hancin dala da ake yi masa har sai an saurari karar da kuma yanke hukunci.

A halin da ake ciki kuma, an dage ci gaba da shari’ar makamanciyar wannan da aka shigar na dakatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa daga binciken wasu kudaden kananan hukumomi da ake zargin sun bata a lokacin gwamnatin da ta shude har zuwa ranar da kotu za ta sanar da ita, wadda mai shari’a S.A. Amobeda ke jagoranta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...