Nasarar Tinubu/Kashim: Lawan Kolo Gaidam ya cancanci yabo – Inji Dr. Sulaiman Isyaku

Date:

DAGA KAMAL UMAR KURNA

 

An bayyana Alhaji Lawal Kolo Geidam a matsayin cikakken Dan kishin kasa Wanda Kuma ya sadaukar da lafiyarsa da lokacin sa wajen zagaye dukkanin jihohin dake arewacin Najeriya domin hado kan Malaman makarantun gaba da sakandire da masana a jihohin domin marawa takarar Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da Kashim Shattima lokacin yakin neman zabe har aka kai ga nasara.

 

Shugaban kungiyar gamayyar Malamai da Masanan ta kasa Dr Sulaiman  Isyaku Muhammad, ne ya bayyana hakan a wajen taron da kungiyar ta shiryawa kungiyoyi irin ta a birnin tarayya Abuja, domin shirya yadda za’a bada lambar yabo ga Alhaji Lawal Kolo Geidam bisa irin gudunmawar daya bada har Shugaba Tinubu da Kashim Shattima suka Kai ga nasara.

Talla

Dr Sulaiman yace samun mutane irinsu Alhaji Lawal Kolo Geidam a tsakanin al’umma abu ne Mai matukar tasiri duba da yadda yake sadaukar da Kansa da komai nasa domin ganin al’ummar arewacin kasar nan sun samu kyakkyawar makoma da ingantacciyar rayuwa daga gwamnatin tarayya.

Da dumi-dumi: Shugabannin Jam’iyyar NNPP 9 Sun Fice Daga Jam’iyyar

Wasu daga cikin ‘yan kungiyoyi daban daban da suka halarci taron bada lambar yabon ga Alhaji Lawal Kolo Geidam sun bayyanawa jami’in yada labaran kungiyar ta Malamai da Masanan dake makarantun gaba da sakandiren kasar nan Kamal Umar Kurna cewa bawa kolo lambar yabon na a matsayin Wani salo na nuna gamsuwa da rawar da ya taka a baya yake Kuma cigaba da takawa har a yanzu domin inganta rayuwar al’ummar jihohi 19 dake arewacin kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarki Aminu Ado Bayero ya baiwa Alan Waka Sabuwar Sarauta a Masarautar Kano

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Mai martaba Sarkin Kano na 15...

Soke Hawan Sallah: Dole Gwamnatin tarayya ta biya mu diyya – Gwamnatin Kano

Daga Isa Ahmad Getso   Gwamnatin jihar Kano ta bukaci gwamnatin...

NiMet ta bayyana jihohin da za a sami tsawa da ruwan sama na kwanaki 3 a Nigeria

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya ta...

Hajjin bana: Gobarar ta tashi a otel din wasu Alhazan Nigeria a Makka

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Hukumar kula da Alhazai ta Najeriya...