Inganta tsaro: Sarkin Kano ya hori Hakimai da Dagatai su marawa Civil Defense Baya

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci Hakimai da dagatai da masu unguwarni su marawa yunkurin Hukumar tsaro ta cikin al’umma baya wato civil Defence domin samun nasarar kakkabe bata gari dake cikin al’umma.

 

Mai Martaba sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yaKe karbar ayarin shugabanin gudanarwar hukumar tsaro ta cikin al, umma Civic Defence bisa jagorancin sabon kwamandan hukumar Muhammad Lawan falala a fadarsa.

Talla

A sanarwar da babban Sakataren yada labaran masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24, yace Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana yunkurin hukumar tsaro ta cikin al’umma da cewa ya dace, duba da ganin irin yadda take gudanar da aikin ta ba dare ba rana.

Da dumi-dumi: Shugabannin Jam’iyyar NNPP 9 Sun Fice Daga Jam_iyyar

Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Daganan sai yaja hankalin daukacin al’ummar jihar Kano su himmatu Wajen gudanar da addu’oi na musamman domin samun cigaban dorewar zaman lafiya a jihar kano dama kasa baki.

Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yiwa sabon kwamandan fatan Alkhairi ayayin gudanar da aikinsa tareda samun nasara.

Tunda farko da yake jawabi, sabon kwamandan hukumar tsaro ta cikin al, umma wato civic Defence, Muhammad Lawan falala, yace sun Kawo wannan ziyarar ne ga Mai martaba sarki domin gaisuwar bangirma tare da neman tabaraki da sanya albarka.

Lawan falala, ya bayyanawa sarkin Kano yunkurin hukumar don haka yake Neman hadinkai da goyon bayan masarautar kano domin samun nasarar cimma burin da akan sanya a gaba na wajen dakile masu aikata miyagun laifuka a cikin al’uma.

A yayin ziyarar dai sabon kwamandan hukumar yana tare da manyan Jami’an gudanarwar hukumar ta jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...