Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaban kasa Bola Tinubu ya kammala shirin kaddamar da dabarun magance matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yamma nan da ‘yan makonni masu zuwa.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a Kano yayin da yake ganawa da manema labarai bayan ziyarar ta’aziyyar rasuwar Abubakar Imam Galadanchi a ranar Lahadi.

Kashim ya bayyana cewa rikice-rikicen da ake fama da su a yankin na da nasaba da talauci da rashin jan al’umma a jika wanda shi ma shugaba Tinubu zai samar da mafita.
Yanzu-Yanzu: Yadda Tinubu zai samar da hukumar kula da farashin abinci a Nigeria
Mataimakin Shugaban kasa ya kara da cewa, shugaba Tinubu na magana ne kan musabbabin duk wani tashin hankali na ‘yan fashin daji da masu tada kayar baya a yankin wanda za a fitar da mafita nan ba da jimawa ba.
“Shugaban kasa ya kuduri aniyarsa na kawo ƙarshe ta’addanci a zamanin mulkin sa.
Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya magantu kan batun Murabus din da ya yi
Kuma rikice-rikicen da muke fama da su a yankin Arewa maso Yamma, wanda ke da alaka da talauci abu ne da shugaban kasa ya kuduri aniyar tunkararsa.
“A cikin makonni masu zuwa zai fito kuma zai kaddamar da wani tsari Mai suna ‘Fulaku’.
Shugaba Bola Tinubu nan da makwanni biyu masu zuwa zai kaddamar da shirin ‘Fulaku’ wanda zai magance korafe-korafe da rashin zaman lafiya da ’yan uwanmu Fulani ke fama ba su a yankin Arewa maso Yamma.