Kwazon Aiki: Wata Kungiya ta Karrama Babban Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Kano

Date:

Daga Abdullahi Sani Doguwa

 

Wata Kungiya ta karrama babban daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kano Alh. Hassan Ahmad Muhammad, a matsayin wanda ya tafiyar da shugabancin hukumar sa yadda ya dace a tsawon lokacin da ya kwashe yana gabatar da aikin sa.

 

Kungiyar marubuta ta Najeriya ce ta bada wannan lambar yabo ga Babban Daraktan bayan nazari da bincike kan aiyukan shugabannin hukumomin kashe Gobara na jihohi, inda suka bayyana shi a matsayin kwararre kuma jajirtacce, wanda ya tafiyar da ayyukan hukumar bisa kwarewa da sanin makamar aiki.

Talla

Jaridar AmazingFm.ng ta rawaito cewa Kungiyar marubutan ta majalisar dokokin tarayyar Najeriyar ta kuma yi kira ga daraktan, daya kara jajircewa a aiyukan jin kai ga al’umma don ciyar da hukumar sa gaba, kasancewar irin su ake bukata a kowace ma’aikata, domin samun ci gaba mai dorewa a kowanne fanni, tare da kira ga sauran ma’aikata da shugabanni Suyi koyi da irin jajircewa da salon gudanarwar sa a rayuwar su ta aiki.

Shari’ar zaɓen gwamnan Kano: Gawuna bai taya Abba murnar cin zabe ba – Rabi’u Bichi ya fadawa Kotu

A nasa bangaren Babban Daraktan Hukumar kashe Gobara ta jihar Kano, Alh. Hassan Ahmad Muhammad, ya bayyana jin dadin sa da wannan karramawa, da alkairin cigaba da jajircewa da kyautata alaka tsakanin hukumar sa jama’a, domin magance matsalolin tashin gobara a kasuwannni da sauran wurare a fadin jihar don kaucewa asarar dukiya da rayukan al’umma.

Alh. Hassan ya bayyana cewa hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta fadad sashen wayar da kai akan matakan kariya ga al’umma inda ya godewa daukacin ma’aikatan hukumar da Gwamnatin Kano bisa goyon baya da take baiwa hukumar don gudanar da aikin ta yadda ya dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...