Daga Hafsat Lawan Sheka
Shugaba ƙasar Nigeria Bola Tinubu yace zai ƙirƙira tare da tallafa wa Hukumar Kula da farashin Kayan abinci ta ƙasa, wacce za ta yi nazari tare da ci gaba da kayyade farashin abinci tare da kula da dabarun Adana abincin a Nigeria.
Mai baiwa shugaba Tinubu shawara na musamman kan ayyuka na musamman, sadarwa, Mista Dele Alake ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a ranar Alhamis, don yiwa al’umma cikakken bayanai game da yadda za’a kula da farashin abinci a Nigeria.

Alake ya bayyana cewa ta hanyar hukumar, gwamnati za ta daidaita magance hauhawar farashin kayayyakin abinci.
Jaridar SaharaReporters ta rawaito cewa, biyo bayan ayyana cire tallafin man fetur da shugaba Tinubu ya yi a ranar 29 ga watan Mayun 2023, da kuma sake fasalin tattalin arziki da ya biyo baya, farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zabi, wanda ya haifar da tsadar kayan masarufi da jefa al’umma cikin mawuyacin hali.
Har ila yau, rashin tsaro a fadin kasar nan, musamman hare-haren makiyaya da manoma wanda ya jawo lalata filayen noma a yankin arewa ta tsakiya da kuma Kudu maso Gabas da suka kori manoma daga gonakinsu ya taimaka matuka wajen matsalar karancin abinci a kasar.
Sai dai a jawabin da ta yi wa ‘yan jaridu kan yadda za ta cim ma shirin ta, fadar shugaban kasar ta bayyana cewa ta tara masu ruwa da tsaki daga hukumar hada-hadar kayayyaki ta kasa (NCX), kamfanonin iri, hukumar kula da iri ta kasa da cibiyoyin bincike, hukumomin bada lamuni na kasa, kungiyoyin samar da kayayyaki da sauransu don tallafawa kokarin shugaba Bola Tinubu don Saukakawa yan Nigeria ta fuskar abinchin.
Alake ya ce, za su hada tsarin tsaron kasar don kare gonaki da manoma domin baiwa manoma damar komawa gonakinsu ba tare da fargabar hare-hare ba.
A wani bangare na dabarun shiga tsakani, fadar shugaban kasar ta ce, “nan take za mu saki takin zamani da hatsi ga manoma ga magidanta domin magance matsalolin da cire tallafin ya haifar a Nigeria.
“Dole ne a samar da hadin kai cikin gaggawa tsakanin ma’aikatar noma da ma’aikatar albarkatun ruwa ta kasa, don tabbatar da isashen tsarin ban ruwa na gonaki da kuma tabbatar da cewa ana samar da abinci a duk shekara ba da Damina kawai ba.
“A matsayinmu na kasa, shugaban kasa ya bayyana karara cewa ba za mu iya wadatuwa da domin Damina kadai ba , dole sai mun inganta noman rani da damina don wadata Kasar nan da abinci.