Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Nigeria NEMA, Ahmed Habib ya shawarci gwamnonin Kasar da su samar da cibiyoyin bayar da agajin gaggawa a jihohinsu domin kare afkuwar ambaliya.
“Idan gwamnonin za su bai wa hukumar haɗin-kai da kuma karɓar shawara, to ba za a iya rage asarar da aka samu a bara”.

Shugaban Hukumar ya bayyana haka ne bayan wani zama da ya yi da wasu gwamnoni a Abuja, babban birnin Nigeria.
Ya kuma bukaci gwamnonin da su wayar da kan mutane kan muhimmancin komawa yankunan da ba su da haɗarin fuskantar ambaliya domin kare asarar rayuka da kuma dukiyoyi da sauransu.
Habib ya kuma ce akwai bukatar a taimakawa hukumar da kuɗaɗe saboda hakan zai taimaka wajen kare afkuwar bala’o’i da za a iya samu.
A makon da ya gabata ne, NEMA ta yi hasashen cewa za a iya samun ambaliya a jihohi14 na faɗin Najeriya sakamakon mamakon ruwan sama.