Tsaftace Kano: Kungiyoyi sun fara karrama Danzago

Date:

Daga Kamal Umar Kurna

 

Shugaban kwamitin karta kwana na kwashe sharar jihar Kano Amb. Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya sha alwashin cigaba da sadaukar kan sa wajen ganin jihar nan ta samu habaka da Samar da kyakkyawan yanayi domin da cewa da manofofin gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusif.

Tallah

Amadu Danzago ya bayyana hakan ne lokacin da kungiyar ‘yan asalin jihar Kano masu tsaftar muhalli suka Mika masa shaidar girmamawa bisa namijin da kokarin da kwamitinsa yayi na kwashe sharar dake jibge a wasu yankunan jihar kano cikin kankanin lokaci.

Hotuna: yadda Sarkin Bichi ya gudanar da hawan ƙarshe

Dan zago yace tsaftace Muhalli da titunan jihar nan nada alaka ta kai tsaye da Samar da ingantacciyar lafiya ga al’umma, a don zai cigaba da bada dukkan lokacin sa wajen kwashe sharar.

A jawabinsa tunda fari shugaban kungiyar Dr. Bala Mohammed yace sun baiwa Dan zago shaidar girmamawar ne duba da yadda cikin kankanin lokaci kwamitinsa ya Samar da yanayi mai kyau a mafi yawan titunan jihar kano.

“Na mijin kokarin da ka yi wajen tsaftace jihar kano shi ne dalilin da yasa kungiyarmu ta amince da baka wannan matsayi na uban kungiyarmu domin samun nasarar da aka Sanya a gaba”. Inji Dr. Bala Mohammad

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...