Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN ta musanta zargin da ake yiwa kungiyar na cewa zata kara farashin man zuwa naira 700.
Shugaban kungiyar na Kudu maso Yamma Dele Tajudden ne ya musanta karin kudin man fetur din a zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN.
Shugaban kungiyar dillalan man fetur din ya bukaci al’umma dasu yi watsi da jita jitar da ake yadawa kan karin kudin man.

Ya ce farashin man fetur ba zai wuce yadda ake sai da shi a yanzu ba.
Idab za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Kungiyar a ranar talata ta ce akwai yiwuwar farashin man yakai Naira dari 6 zuwa 7 saboda karancin samun Dala daga yan kasuwar da suke sayo man daga kasashen waje.