Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Tsohon dan takarar majalisar tarayya kura madobi da garum Malam a jam’iyyar APC Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso ya taya tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da al’ummar jihar kano murnar zagayowar bikin Sallah Babba.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan ne ta cikin wani sako da ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.

” Wannan lokaci ne mai tarin falala da ya kamata mutanenmu na jam’iyyar APC su mai da hankali wajen yin addu’o’i na musamman domin Allah ya baiwa dan takarar gwamnanmu Dr. Nasiru Gawuna da Murtala Sule Garo nasara a Shari’ar da ake yi”. Inji Musa Iliyasu Kwankwaso
Babbar Sallah: Mataimakin gwamnan Kano ya taya Abba Gida-gida, Kwankwaso da Musulmi murna
Musa Iliyasu wanda shi ne Sarkin yaƙin Masarautar Karaye ya taya Mai martaba Sarkin Karaye Dr. Ibrahim Abubakar II da tsahon dan takarar gwamnan kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa a takara Hon. Murtala Sule Garo da Sauran shugabannin jam’iyyar APC da al’ummar jihar kano baki daya murnar Barka da Sallah.

Ya bukaci al’ummar musulmi musamman wadata da su tallafawa masu karamin karfi a wannan lokaci domin Sanya farin ciki a zukatan su don neman dacewa duniya da lahira.