Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Tsohon gwamnan Kano kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, ya ce ya samu wani goron gayyata na musamman daga sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya zuwa birnin New York dake Amurka.
Kadaura24 ta rawaito Malam Shekarau wanda shi ne Sardaunan kano yace da Gaske ne majalisar ta gayyace shi, amma ba’a yi masa cikakken bayani kan dalilin gayyatar ba, amma zai amsa gayyatar a mako mai zuwa.
Yanzu-Yanzu: Abba Gida-gida ya tura sunayen wadanda zai nada a matsayin kwamishinoni
A wani sako da mai taimakawa tsohon gwamnan kan kafafen sada zumunta da daukar hoto Jibril Muhammad Na-Tara ya wallafa ya tabbatar da wannan goron gayyata da aka aikewa tsohon gwamnan na Kano Malam Ibrahim Shekarau.

Yanzu dai abun jira shi ne aji menene dalilin gaiyatar da majalisar dinkin duniyar ta yiwa Malam Ibrahim Shekarau, wata kila idan ya dawo ya yiwa al’umma bayani gane da abubun da suka tattaunawa.