Yadda ‘yan Ƙasar Nijar Mazauna Kano da suuran jihohin Nigeria suka zabi yan majalisun su

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Al’ummar kasar Jamhuriyar Nijar mazauna kasashen ketare sun kada kuri’un su domin zabar ‘yan majalisun da za su wakilce su a gunduma ta 9 a zauran majalisar dokokin kasar.

 

Hukumar zaben kasar (CENI ) ce ta shirya zaben wanda aka gudanar a ranar Lahadi 18 ga watan Yuni 2023, wanda kuma yan kasar mazauna jihar kano suka kada kuri’ar su .

Yanzu-Yanzu: Abba Gida-gida ya sake sabbin nade-naden mukamai

Jagoran hukumar zaben, Alhaji Sa’ad Isufu da ya kula da yadda zaben ya gudana a wasu jahohin Nijeriya da suka hada da Kano, Katsina, Adamawa, Sokoto, Kebbi, Bauchib,Gombe da Kaduna, ya shaida wa kadaura24 cewa, sun duba rumfunan zaben guda 41 kuma kowacce an fara akan lokacin da aka tsara.

Tallah

Ya kara da cewa a jihar Kano akwai akwatinan zabe 12, wadanda ake saran mutane dubu goma sha takwas da tara (1809) ne za su kada kuri’unsu a cikin su.

Ya ce gunduma ta 9, ta kunshi kasashe 19 da suka hada da Nijeriya, Benin, Togo, Faransa, Belgium da dai sauransu.

Shugaban hukumar zaɓen CENI Sa’ad Isufu ya ce ka’idar kundin tsarin zaben shi ne an bayar da awanni 11 domin mutane su je su kada kuri’ursu .

‘’Dalilin da yasa aka dauki wannan matsaya ita ce, wasu kasashen lokacin ba dai-dai yake tafiya ba kamar Nijeriya idan safiya ce wasu kasashen kuma dare ne ko asuba shi yasa aka bayar da awanni 11 ga kowa’’. A cewar Sa’ad Isufu

Ya kuma ce da zarar an kammala zaben za a kirga ba tare da kace-nace ba , inda ya tabbatar da cewa za su jira sauran jahohin da suke da nisa kamar Borno, Sokoto, Kebbi, Adamawa da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...