Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumomi a Kasar Saudiyya sun bayyana cewa an ga jinjirin watan Zulhajj a kasar a wannan rana ta Lahadi, wanda hakan yasa gobe litinin ya zama daya ga watan Zulhajj.
Sanarwar da sashin Haraimain Sharifain ya fita da yammacin wannan rana ta Lahadi, sun nuna cewa za’a gudanar da hawan arfa a ranar talata 27 ga watan Yuni 2023, wanda yayin dai-dai da 9 ga watan Zulhajj 1444 bayan Hijira.
KEDCO sun bayyana dalilin da yasa ake fuskanta rashin wuta a Kano, Jigawa da Kaduna
Sanarwar ta Kuma Kara da cewa Babbar Sallah zata kasance ranar Laraba 10 ga watan Zulhajj dai-dai da 28 ga watan Yuni na shekarar 2023.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a jiya asabar hukumomin ƙasar saudiyya suka bada sanarwar fara duba jinjirin watan na Zulhajj a wannan rana ta Lahadi kamar yadda Nigeria ma ta bada umarnin fara duban watan ta bakin Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’eed Abubakar na 3.