Daga Safiyanu D Jobawa
Tsohon dan majalisar tarayya wanda ya wakilci kananan hukumomin Kura/Madobi/Garun mallam, Hon Kabiru Idris Danhassan ne ya bayyana cewa ba zai taba mantawa da al’ummarsa ba duk da baya kan wata kujerar mulki.
Kabiru Danhassan ya bayyana hakan a wajen mika tallafin Takin zamani a garin Karfi dake karamar hukumar Kura.
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya yi sabbin nade-naden mukamai
Yace ya raba takin don tallafawa manona sakamakon muhimmancin da noma ke da shi a cikin al’umma, musamman a yankin kura madobi da garum mallam.
Dama a baya na raba irin wannan takin lokacin Ina wakiltarku, to yanzu ma da bana wakiltarku ba zan bar ku haka nan ba, zan cigaba da amfani da dan abun da nake da shi waje tallafa muku akan abun da kuka shahara akansa shi ne noma”. Inji Danhassan

Daga bisa ni ya godewa al’ummar wadan nan yankuna bisa sahale masa wakilcinsu a majalisar tarayya, sa’annan ya yi alkawarin cigaba da rike musu amana har tsawon rayuwa. Kuma ya ce zai cigaba da irin wadan nan abubuwan alheri lokaci-lokaci.
Sama da buhu takin-zamani dari-hudu (400) a ka raba wa manoman yankunan na Kura/Madobi/Garun mallam a ranar a jiya asabar .