Daga Kamal Umar Kurna
Shugaban kwamitin kwashe shara na jihar Kano Amb. Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya bayyana cewa nan da kwanaki biyu masu zuwa kwamitinsa zai kammala aikinsa, wanda a yanzu aikin nasu na kwashe sharar yana matakin karshe.
Zago ya bayyana hakan ne lokacin da ake kammala kwashe sharar dake Shahuci daidai police station.
Ɗalibai sun yi zanga-zanga kan garkuwa da yan uwansu a Zamfara
” Tun da gwamna ya dora mana wannan aiki muke shiga lungu da sako na jihar kano domin kwashe tarin sharar da ta addabi al’umma Kuma masha Allah kwalliya ta biya kudin sabulu”. Inji Dan zago
Gwamnatin Kano za ta rushe Masarautun Gaya, Rano, Bichi da Karaye da Kuma dawo da Sarki Sunusi
Amb. Ahmadu Haruna zago ya yabawa daukacin al’ummar jihar kano bisa hadin kai da goyon bayan da suka baiwa kwamitinsu wajen kwashe shara a birnin kano, Inda Kuma yayi kira a gare su da su baiwa dukkanin aiyukan da gwamnatin Abba Kabir Yusuf zata yi goyon baya domin ciyar da jihar kano Gaba.
Shima a nasa jawabin daraktan ayyuka na hukumar kwashe sharar jihar nan Alhaji Sha’aya’u Abdulkadir Jibrin yace rashin isassun kayan aiki ne ya hana su kwashe sharar tuntuni.
“Amma ya yabawa wannan tsari da gwamnatin jihar kano ta bullo da shi wanda zai matukar taimakawa wajen inganta lafiya da rayuwar al’umma kano.”. A cewar Alh. Sha’aya’u Abdullahi

Suma al’ummar da aka kwashe musu sharar dake yankunansu a yau sun bayyana irin halin kuncin da suka tsinci kansu a ciki sanadin jigbe musu sharar wurin da suke rayuwa.
Sun kuma godewa gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Gida-gida bisa fito da wannan tsari na raba kano da tarin shara.
Unguwannin da kwamitin ya kwashe shararsu a yau sun Hadar da Kofar ruwa, Shahuci Dan dawaki police station, Man ladan.