Daga Auwalu Alhassan Kademi
A halin yanzu Sarkin Kano na 14, Khalifa Muhammadu Sanusi II yana ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a fadar gwamnati da ke Abuja.
Sanusi, tsohon gwamnan babban bankin kasa, ya isa fadar shugaban kasa ‘yan mintuna kadan kafin karfe 05:00 na yamma.
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya bayyana ranar da zai mikawa majalisa sunayen kwamishinonini
Ziyarar tasa na zuwa ne mako guda bayan da shugaban kasar ya dakatar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.
Duk da cewa dalilin ganawar tasu bai fito fili ba, amma dukkan mutanen biyu suna ganawa a karon farko tun bayan da Tinubu ya hau kujerar shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu.
Cikakkun bayanai nan ba nan da jimawa ba…