Yanzu-Yanzu: Ginin Daula Otal ya fadawa wasu matasa masu dibar ganima

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Ana zargin wani bangare a ginin Tsohuwar Daula da Gwamnatin Jahar Kano ta rushe ya fada kan wasu Matasa masu diban Rodi.

Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa gwamnatin jihar kano ta rushe ginin da akai a tsohuwar Daula Otal a makwani biyu da suka gabata saboda zargin anyi ginin ba bisa ƙa’ida ba.

Yanzu-Yanzu: Tinubu ya kaddamar da majalisar tattalin arzikin Nigeria

Yanzu haka dai Jami’an Hukumar kashe Gobara da ta bada Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA na yunkurin zakule Mutanen daga baraguzan ginin.

Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya bayyana ranar da zai mikawa majalisa sunayen kwamishinonini

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano SFS Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatarwa jaridar kadaura24 faruwar lamarin.

Ya kuma ce tuni jami’an hukumar su sun Isa wajen domin ceto wadanda lamarin ya faru da su, ya kuma bayyana cewa tuni sun Sami nasarar ceto mutane 3 daga cikin baraguzan ginin.

” Tuni jami’anmu sun ceto mutane uku kuma wadanda lamarin da ya faru a kan idansu , sun tabbatar mana da cewa akwai ragowar mutane da suke ciki don haka muna cigaba da bincikawa,Amma dai har yanzu bamu Sami wanda ya rasa ransa ba”. A cewar Saminu Yusuf Abdullahi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...